Sakataren harkokin wajen Birtaniya yace yanzu haka babu wani shirin ‘kara kai hare-haren soji kan Syria, amma Birtaniya da kawayenta zasu ‘kara ‘daukar mataki in har shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya ‘kara yin amfani da makamai masu guba kan ‘yan kasarsa.
Da safiyar jiya Asabar ne jiragen saman yakin kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya, suka yi lugudan wuta akan wasu cibiyoyin bincike na kimiyya a kasar ta Syria, ‘daya yana babban birnin Damascus, sauran biyun kuma suna kusa da Homs, dake dab da iyakar da arewacin Lebanon.
Jami’an sojin Amurka sun ce duk makaman da aka harba sun sami nasarar sauka inda aka auna su, ta hanyar yin taka tsan-tsan don kauce wa kashe farar hula.
An ‘dauki matakin kai harin ne don mayar da martani ga wani hari da makami mai guba da aka kai garin Douma, wanda ya kashe mutune sama da 40 ya kuma kwantar da sama da mutane 100. Amurka da kawayenta sun zargi sojojin Assad da yin amfani da makamai masu guba. Zargin da Syria da Rasha suka musunta.
Facebook Forum