Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan Kungiyar OPCW Sun Isa Douma Don Bincike


Wani sashin da ya yi kaca-kaca.
Wani sashin da ya yi kaca-kaca.

Nan take dai ba a sami wani maida martani daga kungiyar sa ido akan makaman guba da ake kira OPCW a takaice ba.

Wani gidan talabijin din gwamnatin kasar Siriya ya ce kwararru daga kungiyar dake sa ido akan makaman guba ta kasa-da-kasa sun shiga Douma, inda ake kyautata zaton harin da aka kai wajen, wanda ya kashe mutane dayawa a farkon watan nan na guba ne.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta zargi Rasha da yinkurin hana kwararrun yin bincike akan mummunan harin da aka kai Douma, kusa da Damascus, abinda ya kara dagula al’amura ya kuma hana kwararrun gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

“Ta yiwu Rasha ta yi haka ne saboda ta gano cewa idan wurin da aka kai harin ya dade ba a yi bincike akan sinadiran dake wurin ba, to zasu fara gushewa,” a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert a lokacin da ta yi bayani a gidan talabijin din Alhurra.

Ita kuma Rasha ta dora laifin jinkirin da aka samu akan hare-hare ta sama da Amurka, da Faransan da kuma Burtaniyya suka kai a cibiyoyin hada makaman guba 3 na Siriya ranar Asabar din da ta gabata. Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov shi kuma ya ce kwararrun basu sami damar shiga wurin bane saboda ba su sami izini ba daga hukumar tsaron MDD ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG