Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Shari'ar Amurka Tace FBI Na Sane da Bayanan da Ta Fitar daf da Zaben Shugaban Kasa


James Comey daraktan hukumar FBI
James Comey daraktan hukumar FBI

Jamia’an shara’a na Amurka sun ce jamia’an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI suna sane da wasu Karin sakonnin Email dake da nasaba da binciken da ake yiwa Hillary Clinton da aka gano tun ba yau ba, amma basu ce kome ba sai ranar Juma'ar da ta gabata, Kwanaki 11 kafin a gudanar da Zaben shugaban kasa.

Sai dai abinda ba a gane ba shine dalilan da suka sa Darektan FBI James Comey bai gabatarda wannan bayanin ba sai da ana daf da zaben.

Tun farko dai tawagar kemfen din Hilary da jamiyyar Democrat sunyi murna a cikin watan Yuli lokacinda suka ji Comey yana fadar cewa an kamalla binciken da ake yiwa tsohuwar sakatariyar harkoki wajen Amurka ba tare da bankado wasu ayyukan assha ba.

To sai dai sake tado wannan batu yasa abokin karawar ta na jamiyyar Republican Donald Trump yayi murna da sake jin an bankado wannan batu da hukumar ta FBI tayi.

Wannan ma yasa Trump din ke cewa jefa wa Hillary kuri’a tamkar mika gwamnatin Amurka ne ga ayyukan cin hanci da rashawa wanda zai zame barazana ga ingancin kundin tsarin mulkin kasar ta Amurka.

Wannan batu na Email din na baya-bayan nan, ya sake kunno kai ne a cikin wani sabon binciken da hukumar ta FBI tayi wa tsohon dan majilisar dokokin na Amurka Anthony Weiner, wanda kuma shine tsohon mijin wata babbar mai taimakawa Hillary Clinton, wato Huma Abedin.

XS
SM
MD
LG