Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawarar ‘Yan Takarar Shugabancin Amurka Ta Karshe


Muhawarar Yan takarar shugabancin Amurka
Muhawarar Yan takarar shugabancin Amurka

Jiya ‘yan takaran shugaban kasa a zaben wannan shekara a nan Amurka, Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrats da Donald Trump na jam’iyyar Republican suka yi muhawarsu ta karshe, inda suka gwabza akan batutuwa daban-daban da suka hada da tattalin arziki, harakokin diplomasiya, sha’nin tsaro da inganta rayuwar al’umma.

Daya daga cikin abubuwan da suka fi janyo hankalin wadanda suka kalli muhawar shine dari-darin da Donald Trump ya nuna lokacin da aka tambaye shi ko zaiyi na’am da duk sakamakon da ya fito a karshen zaben nasu, inda Trump yace “zan duba sakamakon a lokacinda ya fito, yanzu bana ganin wannan sakamakon, zan dube shi in ya fito sannan in yanke hukunci.”

A tata amsar, Hillary Clinton tace kasawar Mr. Trump na amsa wannan tambayar game da sakamakon zaben, tana nuna cewa bai cancanta ya zama shugaban kasar Amurka ba, Hillary tace “Ba haka akidar siyasarmu ke tafiya ba, munfi shekaru 240 muna siyasa, muna gudanar da zaben adalci, kuma mukan karbi sakamakon zabe koda bai zo yadda muke so ba.”

XS
SM
MD
LG