WASHINGTON, DC —
A jawabin da yayi jiya Alhamis wajen wani gangamin siyasa na nemarwa Hilary Clitnon, ‘yar takarar shugabar kasa a lemar jam’iyyarsu ta Democrats, goyon baya, shugaba Obama yace tangal-tangal din da Donald Trump yake yi na ko zai amince da sakamakon zaben ko ba zai amince da shi ba, abu ne mai hatsarin gaske ga tsarin siyasar Amurka.
Matsaayin baya-bayan nan da Trump ya dauka gameda batun sakamakon nan dai shine wanda ya gaya wa dimbin magoya bayansa a jiyan, cewa zai amine da sakamakon zaben idan shi aka zaba kawai.
A lokacin muhawarar da yayi da Hilary Clinton jiya a birnin Las Vegas ne, Trump ya girgiza siyasar ta Amurka sadda yaki ya fayyace ko zai yi na’am da duk sakamakon da ya bayyana a zaben, inda yace ya fi son ya kyale kasar ta zauna cikin abinda ya kira “jiran tsammani.”