Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Sabon Filin Jirgin Sama Na Senegal Suna Yajin Aiki


Ma’aikatan da ke kula da zirga-zirgan jiragen sama na sabon filin saukar jiragen saman kasar Senegal sun shiga yajin aiki ‘yan kwanaki da bude filin saukar jiragen.

A jiya Juma’a an soke duk wani tashi da saukar jirage a filin jirgin saman na birnin Dakar, bayan da ma’aikatan dake kula da jiragen suka bayyana shiga yajin aiki na kwana guda.

Ma’aikatan dai sunce suna yin yajin aikin ne domin su kare lafiyar matafiya, saboda ba a basu cikakken horo ba kafin bude filin jirgin saman.

“A kwai sababbin kayayyakin aiki na zamani an saka. Amma ba a horar da mu yadda zamuyi aiki da su ba,” a cewar Mame Alioune Sene, shugaban kungiyar ma’aikatan.

Sabon filin jirgin saman wanda aka kashe dala miliyan 680 wajen gina shi, an bude shine ranar 7 ga wannan wata na Disamba, bayan da aka yi jinkirin tsawon shekaru 10.

Gwamnatin kasar ta ce filin jiragen zai sa kasar Senegal ta zama wajen zuwan masu yawan bude ido a yammacin Afirka.

Jami’an filin jiragen dai sunce an soke tashin jirage kusan 30 saboda yajin aikin ma’aikatan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG