Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mugabe Ya Je Jinya A Singapore


Tsohon Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe
Tsohon Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe

Biyo bayan murabus din da shuga Mugabe yayi daga kujerar shugaban kasa, sai gashi an gano shi a Singapore wanda akace yaje asibiti ne

Tsohon mai magana da yawun Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbabwe mai murabus yace shugaban na kasar Singapore a halin yanzu domin duba lafiyar shi.

An ga shugaba Mugabe a yayin da yake barin wani asibiti a Singapore a yau jumma'a. Tun bayan da yayi murabus wanda ya kawo karshen mulkin sa na shekaru talatin da bakwai ba'a sake ganin shugaban dan shekara 93 a bainar jama'a ba. Ana zargin tsohon shugaban da laifin mulkin kama karya, tare da tarwatsa tattalin arzikin kasar. Yana fama sosai da laulayi, inda har aka ce yana fama ne da cutar sankara ko daji.

Mugabe ba zai samu hallartar babban taron jam'iyyar shi ba a birnin Harare wanda za,ayi Jumm'a inda za'a tsayar da wanda ya maye gurbin shi wato Emmanuel Mnangagwa a matsayin dan takarar shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG