A kasar Saliyo, wasu ma’aikatan lafiya biyu da suka warke daga cutar Ebola sun yi karar gwamnatin kasar suna zarginta da sakaci lokacin da ake fama da annobar Ebola.
Ma’aikatan lafiyan dai sun zargi gwamnati ga rashin samar da kayayyakin aikin da suka kamata, har ta kai ga cewa sun kamu da cutar kuma dayawa daga cikin abokan aikinsu sun mutu. Karar da suka shigar na zargin cewa, barnata kudaden da aka samar na yaki da cutar da gwamnati ta yi kai tsaye ya hana su damarsu ta samun rayuwa mai cikakkiyar lafiya.
A shekarar 2013 ne kwayar cutar Ebola ta yadu a kasar Guinea, kuma ta warwatsu zuwa makwabtan kasashe irinsu Laberiya da Saliyo. Sama da mutanen dubu 3 ne suka mutu a Saliyo, haka kuma sama da mutane 11,300 ne suka mutu a duniya, wanda yawancin mutanen daga kasashen yammacin Afirka uku suke.
Gwamnatocin kasashe da kungiyoyin agaji sun taimakawa kasashen yammacin Afirka da Miliyoyin dalar Amirka don a dakatar da yaduwar cutar, amma akwai zargin cewa kasashen da abin ya shafa su uku sun yi sakaci da kudaden da aka basu.
Ma’aikatan kiwon lafiya na Saliyon dai sun shigar da ‘karan gwamnatinsu ne a kotun kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS dake a babban birnin Najeriya Abuja.
Facebook Forum