Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Jam;iyyar dake Mulkin Zimbabwe Ta Gyara Tattalin Arziki - Mnangagwa


 Emmerson Mnangagwa, shugaban Zimbabwe
Emmerson Mnangagwa, shugaban Zimbabwe

Yayin da yake yiwa 'yan jam'iyyarsa ta ZANU-PF, sabon shugaban Zimbabwe ya ce dole ne jam'iyyar dake mulki ta gyara tattalin arzikin kasar da ya yi shekara da shekaru a komade

Yau Juma'a sabon shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce ya zama wajibi jam'iyyar ZANU-PF dake mulkin kasar ta fara gyara tattalin arzikin kasar idan har tana son ta ci zaben shugaban kasa mai zuwa.

Shugaban ya yi jawabi ne a wurin taron kolin jam'iyyar inda ta ja layi tsakanin mulkin yanzu da na tsohon shugaban kasa Robert Mugabe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito

Jam'iyyar ta kori matar tsohon shugaban Grace Mugabe da mukarrabanta kana ta tabatar da sabon shugaban a matsayin dan takararta daya tilo.

Inji shugaban, zamu iya cin zabe idan mun iya nunawa jama'a mun fara farfado da tattalin arziki. Haka kuma zamu iya farfado da tattalin arzikin gaba daya idan mun ci zabe.

Tattalin arzikin Zimbabwe ya komade a shekaru takwas da suka shude cikin shekaru 37 da Robert Mugabe ya yi yana mulki. Hakan ko ya faru ne sanadiyar kwace dubban filaye da karfi da yaji daga hanun turawa manoma wadanda suka mallaki manyan gonakin kasuwanci. (Kamfanin Reuters)

Kasar na iya gudanar da zaben shugaban kasa a watan Maris din shekara mai zuwa, wato 2018.

Shugaba Mnangagwa dan shekaru 75 da haihuwa ya ce "Tsarin Dimokradiya ya tanadi cewa jam'iyyar ZANU-PF ta shiga takarar neman shugaban kasa da jam'iyyun hamayya a zabe mai inganci da adalci da aka yi a bayyane" a bayanin da ya yi a tsakiyar birnin Harare.

Tun farko a watan jiya sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya ce duk wani taimakon kudi da za'a ba kasar domin ta biya bankin duniya da bankin raya kasashen Afirka domin ta daidaita kudin kasarta, ya ta'allaka ne da ci gaban dimokradiya.

A wani yunkurin karfafa matsayin sojoji a siyasar kasar, Shugaba Mnangagwa ya saka wasu janarori uku cikin majalisar kolin kasar akan harkokin mulki wadda kuma ita ce mai yanke shawara a kwamitin kolin ZANU-PF kwatankwancin ta kasar Rasha

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG