Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa ta Amurka ta yi gargadin karuwar hadarin gobara a yankin saboda hadewar bushewar itatuwa da ke kara iza wutar da yanayin zafi.
A jihar South Cariline, gwamna Henry McMaster ya ayyana dokar ta baci a ranar Lahadi, don tallafawa kokarin kashe gobarar, sannan dokar hana kone abu a fadin jihar na ci gaba da aiki.
Ma’aikatan suna kokarin shawo kan gobarar a Dajin Carolina da ke yamma da wurin shakata na gabar teku wato Myrtle Beach, inda aka umarci mazaun yankin da su kauracewa unguwanni da dama, a cewar Hukumar Kashe Gobara ta Gundumar Horry.
Hukumar Kula Da Gandun Daji Ta South Carolina ta kiyasta da tsakar ranar Lahadi cewa gobarar ta kona kimanin murabba’in kilomita 4.9 ba tare da kashe ko kadan ba.
Jami’ai sun ce babu wasu gine-gine da gobara ta kona kuma ba a samu rahoton jikkata ba ya zuwa safiyar ranar Lahadi.
Jami’an kashe gobara na gundumar sun ce ana sa ran jami’ai 410 za su ci gaba da kasancewa a wurin har sai an kashe wutar.
Ana sa ran za a ci gaba da kwashe mutane a ranar Lahadi, kuma jami’ai sun gargadi mazauna yankin dajin Carolina da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana da jakunkunansu idan akwai bukatar kwashe mutane a yankunan su.
A jihar North Carolina, Hukumar Kula da Gandun Daji ta Amurka ta ce ma’aikatan kashe gobara na aiki don shawo kan gobarar daji da dama da ke ci gaba a wani wuri mai girman sama da hekta 161.87, a cikin dazuzzuka hudu a fadin jihar a ranar Lahadi.
Wuri mafi girman shine Gandun Dajin Uwharrie National inda kusan eka 300 ya kone, da kuma kusan kilomita 50 a gabas da Charlotte.
Karamin garin Tryon da ke kudu maso yammacin gundumar Polk ajihar North Carolina, ya bukaci wasu mazauna yankin da su fice a ranar Asabar yayin da gobarar ke bazuwa cikin sauri a can. A ranar Lahadi, jami’ai sun ce ana ci gaba da aikin kwashe mutanen.
Sai dai har yanzu jami’ai ba su bayyana abin da ya haddasa gobarar ba.
Dandalin Mu Tattauna