Hukumomi a California sun ba da sanarwa ga al’ummomin da ke daura da Castaic Lake da su fice daga yankin, bayan da wata sabuwar gobarar daji ta tashi a tsaunukan arewacin Los Angeles.
Kudancin California yana fama da tashin gobara saboda busasshiyar Iska da rashin samun ruwan sama.
Sannan hukumomi sun yi kira ga al'ummar yankin da su kaurace wa kusa da yankin saboda shakar gurbataccen hayaki.
A halin da ake ciki, akwai gargadi game da yiwuwar tashin wata mummunar gobarar a kudancin California.
Dr. Talatu Bako 'yar Najeriya da ke zaune a Los Angeles, California ta shaida wa Muryar Amurka cewa gobarar ta yankin Castaic Lake ta yi barna sosai, kuma hukumomin kashe gobara su na ta fafatawa wajen shawo kanta.
Saurari tattaunawa da Helen Bako cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna