Duk matashin da yake so a dama da shi a harka ta siyasa, wajibi ne ya nemi ilimi, yana da aikin yi kuma ya kasance mai hagen nesa ga kasarsa. Shugaban sashen nazarin illimin sanin harkokin siyasa a jami'ar Bayero ta Kani, yace galibi dai yawan matasa basu da wadannan cancanta.
Sau da yawa matasan da suke shiga harka ta siyasa basu da wadannan fahimta, kuma akasarinsu suna da iyayen gida da suke bin duk abinda suke su yi, ba abun da ya dace ko can-canta ba.
Matasan da ake da su wadanda suke son suyi tashin kawara ne,su sami kudi ta farat daya kamar yadda iyayen siyasa ke yi, ko da yake akwai lokutan da akan samu matasa da ko ta ina sun cancanta, amma da zarar sun fara wani hobbasa sai a tade su.
Farfesa Habu Fagge, ya ce duk da cewar an rattaba hannu akan wannan dokar na Not too young to run da ake ta kururwar cewar an sa hannu, kuma za’a bawa matashi ko matashiya damar takara a kuma yi goggaya da su.
Wani salo ne na burumburum ko da matasan sun fito lallai zasu kasance suna da iyayen siyasa, maimakon a basu cin gashin kansu, na aiki bisa kishin da suke da shi ga kasarsu.
Ya ce matasa a yanzu basu kamo hanyar kawo canjin da ake bukata ba ta fannin sanin madafian iko, ko hangen nesa da sauransu ba.
Facebook Forum