Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Kalaman Batanci Ya Sa Na Fito Da Sabuwar Waka - Double Haske


Masu iya Magana kan ce suna linzami a farkon fara waka ta a lokacin akwai kuruciya sai na sawa kaina suna’ Double trouble’ amma a yanzu dole na sauya sunan ya koma ‘Double haske sakamakon da zarar na shiga cikin al’umma aka tambaye ni suna ina cewa ‘Double trouble sai mutane su fara darewa hakan ce ta sa dole na canza sunana inji mawakin hip-hop Nuradeen Abubakar

A wakokina na hip-hop ina duba matsalolin da ke ciwa mutane tuwo a kwarya mussamam ma a yanzu da ake kokarin magance kalamun batanci wato hate speech, akan hake ne ma na fito da wata sabuwar waka mai suna Zagi

Baya ga wannan matsala ma double haske yayi waka akan auren dole, matsalolin fyade, ciwon yoyon fitsari da matsalolin shan kwaya tsakanin matasa.

Har yanzu mawakan hip-hop bata mike ba a cewar Double haske sakamakon al'umma bata karbi hip-hop kamar yadda aka karbi masa’antar fina-finai ba, ya kara da cewa har yanzu ana yi masu kallon mutane marasa da’a da tarbiya.

Ko da yake acikin mawakan, Nuradden ya ce akan samu wasu mawaka da suke dan kauce hanyar da dole a yi masu kallon marasa da’a.

Waka a yanzu dai bata kawo kudi yadda ya kamata, mawaka basa samun talluka daga kamfanonin kamar yadda aka fara samu a lokacin da wakokin hip-hop suka shigo.

Mawakan hip-hop basu da kungiya kamar kowacce sana’a wanda yana daya daga cikin kalubalen da mawaka ke fuska wanda har kawo yanzu suka kasa kawo maslaha ga kalubalen da suke fuskanta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:11:28 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG