Alhaji Haruna Insha Allah shugaban kungiyar a kasa a tsare a raka a jira ‘For Buhari da Osinbajo 2019’ reshen jihar Kano, ya ce duk mai akidar gina kasa ko gina al'umma tsayawa yake a inda yake, ba ya rika canza sheka ba wato sauyin jamiyya ba.
Ya bayyana haka ne a yayin zantawarsa da wakiliyar DandalinVOA a Kano, inda yake cewa tsayawa a jam'iyya daya shine ke tabbatar da cewar wannan dan siyasar ya tsaya tsayin daka, akan akidarsa ta neman cigaban kasa ko al'ummarsa.
Ya kara da cewar siyasa a yanzu ta zama kasuwar bukata duk inda wasu 'yan siyasa ke tunanin zasu samu kaiwa ga nasara nan suke karkata, kamar yadda masu iya magana kan ce, ta inda baki ya karkace nan yawu ke zuba.
Amma yana ganin yanzu matasa sun farga hatta, wasu jam'iyyun ma sun ankara a yanzu, an fara tawaye ga ire-iren wadannan 'yan siyasa masu kasuwar bukata.
Alhaji Haruna, ya ce matasa suna da kaso kusan saba'in cikin dari na alummar Nijeriya, daga cikin kalubalen da suke fuskanta shine matasan sun koma gefe sakamakon siyasar kudi da suke sanya kansu maimakon akidar su a da.
A yanzu kuwa sun tashi daga dogon baccin da suke yi, kuma matasa na yunkurin tsayar da dan takara matashi mai jini a jika, a zabe mai zuwa wato nan da shekaru biyar masu zuwa.
Facebook Forum