Abdullaziz Abubakar wanda aka fi sani da Abdullaziz E-Z. ya ce ya fara aikin furodusin na fim, ganin cewar ya taso ya tarar da yayyinsa na harkar ta fim, kuma sai ta kasance yadda wasu iyaye ke barin 'ya'yansu ba kwaba harma su kai ga lalacewa saboda gata.
Hakan ne yasa Abdul'aziz shirya wani fim mai suna rayuwar "Rayuwar Dan Auta" wanda yake fadakar da al’umma da iyaye illar barin ‘yayansu ba tare da ana kwabarsu ba, da zarar suna aikata wasu ayyukan alfasha da rashin tarbiyya.
Matashin ya ce a fim din "Rayuwar Dan Auta" na nuna yadda ake shagwaba yara, kuma hakan yake jefa su ga miyagun dabi'u kamar shan kwaya, dama sauransu.
A yanzu ya fi mayar da hankali ga harka ta editin fina-finai da suke hadawa, wanda ke nuna cewar akan samu wata 'yar matsala inda wasu lokutan masu shirya fim ke gardama mussaman ma a wasu lokutan akan samu akasi na rashin daidaito mafi yawa a wajen sa sutura a fannin jarumai.
Daga karshe ya bayyana cewa akan nuna jarumi ko jaruma da kaya kala daban da zarar sun shiga daki ko sun fito a rana daya, an ga sauyin kaya wanda kuskure ne me dauke da sakaci.
Facebook Forum