Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Jihar Adamawa Ta Yiwa Mutane Fiye da Dubu 45 Rajista


Jerin masu neman yin rajistan zabe a jihar Adamawa
Jerin masu neman yin rajistan zabe a jihar Adamawa

Hukumar zabe a jihar Adamawa na cigaba da rajistan wadanda basu yi rajista ba da can ko kuma yanzu ne suka kai shekarun yin zabe kafin lokaci ya kure duk da cewa wasu 'yan siyasa na anfani da wasu matasan su yi rajista fiye da sau daya

Adadin mutanen da suka cancanci kada kuri’a dubu arba’in da biyar da casa’in da biyar ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa dake jihar Adamawa ta yi wa rajiista, daga cikin wannan adadin a karon farko harda masu nakasar hanu daya da kuturta, a na kasa da makonni biyu da dakakatar da aikin rajistar na wucin gadi.

Babban sakataren gudanarwa na hukumar a jiha Alhaji Salihu Ya’u ya ba da wadannan alkalumma ga taron ‘yan jarida a Yola yana bayanin shelkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta amince da karin cibiyoyin rajistar masu kada kuri’a goma bayan ta yi la’akari da matsalar Boko Haram da ta tilastawa mutanen kaura daga muhallansu da kuma fadin wasu kananan hukumomi dake da cibiyar rajista daya .

Shugaban kungiyar mutane masu bukata ta musamman ta kasa reshen jihar Adamawa Malam Abubakar Hosere ya tabbatarwa Muryar Amurka cewa hukumar ta bude rajista wa nakasassu masu hanu daya da kutare a duk cibiyoyinta akasarin abinda ya abku a zabubbukan da suka gabata da ya yi sanadiyyar hana ‘ya’yan kungiyar sama da dubu sittin rasa yin zabe har ya kai ga zanga-zangar nakasassu a jihar.

Amma sai dai babban sakataren gudanarwar ya ce hukumar ta fuskanci kalubalen na rashin kwararrun ma’aikata da kuma yunkurin wasu ‘yan siyasa na kokarin gurgunta shirin ta hanyar anfani da matasa wajen yin rajista fiye da sau daya da niyyar magudin a zaben 2019 mai zuwa, sannan akwai rasihin fahimtar rukunin wadanda aka tsara wa shirin aikin rajistar domin su.

Alhaji Salihu Ya’u ya ce hukumar ta tanadi hukuncin tarar naira dubu goma ko daurin shekara daya ko kuma duka ga wadanda suka sabawa dokar tsarin zabe. Akwai hanyoyin, inji jami’in,na gano masu yin rajista fiye da sau daya ta yadda yin haka zai hana su yin zaben gaba daya.

Hukumar ta sa ran dakatar da aikin rajistar na wucin gadi ranar ashirin ga watan nan domin ta sami damar lika jerin sunayen wadanda suka yi rajista don tantancewa da kuma raba sabbin katunan rajistar ga wadanda aka yi wa. Za a ci gaba da aikin rajistar nan gaba har kamin zabe na 2019.

Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG