Magoya bayan Sanata Ahmed Makarfi bayan da kotun koli ta tabbatar masa da shugabancin PDP sun barke da murna kuma hakan ya kawo karshen shugabancin Sanata Ali Modu Sheriff.
Mai shari'a Bode Rode na kotun koli yace Sheriff ya shigar da kararraki goma a kotuna domin jawowa Makarfi illa sakamakon nadashi shugaban riko a taron Fatakwal.
Makarfi da 'yan jam'iyyar suka yi masa zobe sun nuna sun tsira daga jiwon hawan jini da ya kamasu, ya nuna farin ciki. Yana mai cewa sun gode wa kotun da nuna gaskiya da kuma 'yan jam'iyya da suka jimre har zuwa wannan lokacin. Yace ba zasu bi mutane da bita da kulli ba. Zasu yi kokari su kawo hadin kan 'yan jam'iyyar, da hadin kai ta fannin dimokradiya. Yace ba zasu bi hanyar daukan hakkin wani su ba wani ba.
Jagoran garanbawul ga PDP Shehu Gaban yace yanzu kam burinsa ya cika. Yana mai cewa babu wanda ya kaishi murna a Najeriya yau saboda shi ya fara yaki da Shariff. Yace shi ya fara cewa ba'a bi doka ba.Yana mai cewa dashi aka kafa jam'iyyar tun farkonta.
Bala Bello Tunka daga bangaren Ali Modu Sheriff yana cewa babu jam'iyyar da bata da matsaloli irin nata amma zasu amince da abun da kotun koli ta yanke su kuma yiwa kansu hukumci. Zasu bi abun da shugabanninsu suka fada.
Da yawa cikin magoya bayan Sanata Ali Modu Sheriff basu halarci kotun ba tamkar sun san irin hukumcin da za'a yanke. Mataimakin Ali Sheriff Kairo Odigbo ya fito daga kotun yana murmushi.
Mai ba PDP shawara ta fuskar shari'a a bangaren Ali Modu Sheriff Barrister Bashir Maiduhu yace komi yayi farko zai yi karshe. Yana mai cewa a siyasa ko shari'a ko ka ci ko ka fadi. A wannan halin duk wanda ya ci daidai ne. Yace zasu basu goyon bayan da suke bukata don su yi nasara.
Tun farko Sanata Ali Modu Sheriff na cewa matsa masa aka yi ya shiga shugabancin PDP. Yace yayi gwamna shekara takwas kuma yayi sanata sau uku. Yace a rayuwarsa duk abun da yayi bashi da maigida a siyasa amma yana da yaran siyasa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum