Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Limamin Wata Mijami'a Dake Gyamar 'Yanluadi a Amurka ya Rasu


Taron kungiyar 'yan luadi da madigo
Taron kungiyar 'yan luadi da madigo

Limamin Wata Mijami'a dake Gyamar 'Yanluadi a Amurka Ya Rasu

Allah Ya yiwa wani fitaccen pasto anan Amurka mai suna Fred Phelps rasuwa, paston yayi kaurin suna wajen kyamar ‘yan luwadi. Fred Phelps da magoya bayansa daga wata karamar majami’a sunyi fice wajen zanga zanga a wuraren janan’iza da tarurruka.

Kakakin cocin na Baptist dake Topeka cikin jihar Kansas, yace paston dan shekaru 84 Allah yayi masa cikawa cikin daren laraba. Bai bada dalilan mutuwarsa ba.

Paston ya kafa cocin ne a 1955 inda ya girka majami’ar kan irin zazzafar akidarsa. Galibin ‘yan cocin dangi daya ne walau ta jini ko auratayya.

Karkashin jagorancin Phelps, ‘yan cocin suna wa’azin cewa duk wata musiba data aukawa Amurka, daga bala’o’I kamar ambaliyar ruwa ko wuta ciki harda harin da wani dan bindiga ya kai wata makarantar firamare da ake kira Sandy Hook a jihar Connecticut a ranar 14 ga watan disemban 2012, har ya kashe yara da malamai 26, duk irin wadannan hukunci ne daga Allah saboda Amurka ta yarda da luwadi.

Pasto Phelps da magoya bayansa suna zagaya Amurka, suna zanga zanga a wuraren jana’izar wadanda suka kamu da cutar kanjamau da sojoi da aka kashe a Iraqi da Afghanistan, da kuma zanga-zanga a wuraren da ake bukukuwan makada da mawaka, da taron bada lambobin yabo na ‘yan wasan kwaikwayo da ake kira Academy Awards.

A irin wadannan zanga zangogin, za a ga ‘yan cocin ciki harda yara kanana suna rike da kwalaye da aka rubuta cewa “Allah Ya tsani ‘yan luwadi” da kuma “mun godewa wa Allah da mutuwar wani soja”.
XS
SM
MD
LG