A jiya jumma’a shugaban ya bayyan jerin sauye sauye, da suka hada da kusan dakatar da shirin leken asiri kan shugabannin kasashen waje da suka kasance kawayen Amurka. Kuma daga yanzu bangaren shari’a zai rika sa ido kan tattara bayanan kiraye kirayen da miliyoyin Amurkawa suke yi ta woyar tarho.
Yace gwamnati zata ci gaba da tattara wadan nan bayanan har zuwa karshen watan Maris, daga nan zata mika hakkin adana su ga wata kafa da ba tantance ba tukun bayan da aka nemi shawarwarin bangaren malajisun dokoki.
Mr. Obama ya bayyana wadan nan sauye sauyen ne a cikin jawabi da yayi da aka juma ana dako, sakamakon fallasar dumbin bayanai na hukumar leken asirin da wani tsohon ma’aikacinta Edward Snowden yake yi cikin watanni masu yawa da suka wuce.
Hukumar leken asiri ta na’urori tace Snowden ya saci kasidu milyan daya da dubu dari bakwai da suka kunshi bayanan sirri kamin ya tsere inda ya sami zaman mafaka a Rasha.
Wasu daga cikin kasidun sun nuna Amurka ta saci sauraron kiraye kirayen shugabannin kasashen da suka kasance kawayen Amurka da suka hada har da shugabar Jamus Angela Merkel. Hukumar zata daina yin haka sai dai idan akwai wata damuwa da ta shafi tsaron Amurka.
A cikin jawabin da yayi na tsawon minti 43 jiya jumma'a, Mr. Obama yayi kokarin daidaita bukatar Amurka na tattara bayanai da zasu taimaka wajen wargaza makarkashiyar kawo mata hari shigen wanda aka yi a shekara ta 2001 a New York da Washington,har mutane kusan dubu uku suka halaka, da kuma damuwar cewa shirin leken asirin yana keta ‘yancin walwala da sirrin Amurkawa.