Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi Jawabi Kan Halin da Kasar ke Ciki


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi jawabi akan halin da kasar ke ciki jiya Talata, tare da jinjina wa sojojin Amurka da baraden yaki, tare kuma da shan alwashin ganin cewa, an ba su dukkannin hakkokin da suka cancanci samu.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi jawab kan halin da kasar ke ciki jiya Talata, tare da jinjina wa sojojin Amurka da baraden yaki, tare kuma da shan alwashin ganin cewa, an ba su dukkannin hakkokin da su ka cancanci samu.

Musamman ya jaddada misalin abin da wani soja ya fuskanta, wanda saura kiris wani bam din da aka dasa a gefen hanya a Afghanistan ya hallaka shi, wanda har yanzu ya ke kokarin murmurewa.

Shugaba Obama ya ce mata da maza irin wancen sojan -- mai suna Cory Remsburg -- na tunatas da kasar a har kullum cewa, ba fa da sauki aka gina Amurka ba.

To amman cikin sama da shekaru 200, a cewar shugaban kasar, kasar ta jingine kurakuranta da bacin ranta don ta mika gaba -- a ta bakinsa, "don a kirkiro a gina a kuma fadada damar da kowa ka iya samu na cigaba; don a kubutar da sauran kasashe daga danniya da tsoratarwa. A kuma yada adalci da daidaito da kuma rashin nuna banbanci a karkasin doka."

Ya kuma kammala ne da kalma ta hadin kai; da cewa kasar da Amurkawa ke hankoro ga 'ya'yansu, aba ce da ake iya samu, muddun aka hada kai.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG