Jami'in dake kula da shirin a Najeriya Mr. Michael Habey ya sanarda hakan a wajen bikin kammala yarjejeniyar inganta ilimi a jihohin biyu da aka gudanar a Bauchi. Yace irin wannan aikin ba zai ci nasara ba ba tare da shugabanci na gari ba a tsakiya. Yace jihar Bauchi ta ci sa'a domin ta samu jagorancin kwarai daga sama inda gwamnan jihar ke tallafawa. Yace a fannin ilimi a jihohin Bauchi da Sokoto cikin shekaru biyar da suka wuce an kashe dala miliyan 43.
Abdullahi Dabo shugaban hukumar ilimi a jihar Bauchi ya bayyana irin taimakon da jihar Bauchi ta samu. Tallafin ya taimaka masu wurin inganta ilimin almajirai. Sun kuma ba yara marasa galifu hanyoyin koyan sana'o'i daban daban. Wadanda suka koyi sana'o'i sun basu jari domin su cigaba da abun da suka koya su kuma samu su tsaya da kafafunsu su sami rayuwa ingantacciya.
Gwamnatin Bauchi tace zata cigaba ta dora kan abun da USAID ta bari. Yace hukumar tayi masu tanadi sosai domin su samu su cigaba da irin abubuwan da suka shuka.
Hajiya Yelwa Abubakar Tafawa Balewa babbar darakta a hukumar yaki da jahilci a jihar Bauchi ta yi bayanin irin tallafin da aka basu. An basu tallafi kan koyon karatu da sana'o'i musamman na yara mata.