Ministar kiwon lafiya a Kenya Susan Nakhumicha ta ce yanzu likitocin za su maida hankali wurin kula da marasa lafiya.
Ina kira ga dukkan mu yanzu mu mayar da hankali kan aikin mu. ‘Yan kasar sun kwashe kwanaki 54 suna jira su ga kun koma baki aiki, kuma suna da ‘yanci su bukaci ganin an basu kulawa ba tare da bata lokacin ba.
An cimma fahimtar juna ne bayan tattaunawa ta tsawon makwanni da kuma daukan damarar shiga kotu. Gwamnati da kungiyar likitocin sun amince kan samar da hanyar da ta fi dacewa a biya su da kuma inganta yanayin aikin su.
Shugaban kungiyar hadakar kungiyoyin likitocin Kenya, da masana kimiyar hada maganguna likitocin hakori, Dhavji Atelleah, wanda ya sanya hannu a madadin kungiyar mai mambobi sama da dubu 7, ya ce akwai wata bukatar da ba a biya musu ita ba, amma dai za su ci gaba da fafutukar an kula da kananan likitoci da suke cikin makaranta.
Mun dace a cikin kwanaki 60 ba za a tura su wurin aiki ba, amma dai za mu ci gaba da tattaunawa a kan batun, wanda hakan ke nufin cewa yayin da ake duban batun da ya janyo yajin aiki, za mu yi ta Magana kuma a kan wannan, amma dai abu daya da dole mu tabbatar shine kowa da kowa da kowane likita, da duk mutum da yake da haki a wannan yarjejeniyar da aka cimma tare za a kare muradunsa, kana za mu ci gaba da kare su a kowane lokaci.
Damuwar wasu likitocin ya samo asali ne tun daga wata yarjejeniyar 2017, wadda ta yi batun Karin albashi, da kuma batun inshorar kiwon lafiya ga likitoci da iyalansu da kuma batun alawus na hadari da ayyukan gaggawa.
Gwamnati tarayya da gwamnoni kananan hukumomi sun ki aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar saboda matsalolin kudi da kuma tsoron cewa wasu sassa za su bukaci irin kudade ga ma’aikatansu.
Aisha Hassan wata mai fafutukar kiwon lafiyar al’umma ce a Nairobi. Ta ce komawar likitocin bakin aiki a cibiyoyin lafiya zai taimakawa marasa lafiya.
Muna godiya ga likitocin da wannan shawarar da suka yanke ta komawa asibitoci su taimakawa marasa lafiya, saboda babban kalubale ne aka fada a lokacin da suka kauracewa asibiti.
Marasa lafiya da dama sun mutu, kana wasu basu samu Magani ba, kamar masu cutar kanjamau da masu tarin fuka. Muna da ayyuka da dama da za mu yi saboda yanzu ya kamata mu je mu bibiyi marasa lafiyar. Ko su kansu marasa lafiyar, yana da kyau a taimaka musu.
‘Yan kasar Kenya suna zaton wannan yerjejeniya za ta warware baki dayan rashin fahimtar likitoci da gwamnatin, koda yake ya zuwa yanzu ana ci gaba da tattauna batun daukar kananan likitoci dake cikin makaranta.
Dandalin Mu Tattauna