Sakataren Tsaron Amurka Leon Panetta yana gargadin cewa Isra’ila tana ci gaba da zama saniyar ware a gabas ta tsakiya a lokacinda guguwar canji ta kada a fadin a bana.
Ya fada jiya lahadi kan hanyarsa zuwa Isra’ila a ziyararsa ta farko tun zama babban sakataren tsaron Amurka cewa tilas Isra’ila ta sake farfado da shawarwari da Falasdinawa, kuma ta maido d a hulda tsakaninta d a Masar da Turkiyya.
Panetta wadda ake sa ran zai gana da PM Isra’ila Benjamin Netanyahu d aministan tsaro Ehud Barak yace zai tambayi shugabannin Isra’ila ta hanyoyin da Amurka zata taimaka musu ta inganata danganataka a yankin ganin irin sauye sauye dake faruwa. Haka kuma babban jami’in tsaron Amurkan zai gana da shugaban yankin falasdinu Mahmud Abbas d a PM yankin Salam Fayyad.
Daga bisani Mr. Panetta zai wuce Brussell domin ya halarci taron kungiyar kawancen tsaro ta NATO.
Panetta yace yana da muhimmanci Isra’ila ta nemi hanyoyin tuntuba da wasu kasashe dake yankin domin zaman lafiyarta,kuma Isra’ila tana iya barazana ga tsaronta idan bata nemi mu’amala da wasu kasashe dake yankin.
Haka kuma yace akwai bukatar Isra’ila da Falasdinu su jingine gindaye sharadi su koma teburin shawarwari.