Wakilin Murya Amurka ya zagaya wata kasuwa mai suna Kasuwar Jemage inda ya zanta da wasu da suka je sayen kaya. Wata ta ce tun kafin a fara azumin kaya sun fara tsada. Basu tabuwa. Ta ce to yaya ke nan za'a yi. Wani kuma cewa ya yi to yaya za'a yi tun da ance sai an kawo kaya daga kasashen waje? A ganinsa shi yasa kaya ke tsada. Wasu kuma sun zargi 'yan kasuwan da boye kayansu sai sun fahimci cewa mutane sun matsu gap da kama azumi kana su fitar dasu su kuma sayar da tsada.
Wani malamin addin cewa ya yi boye kaya da kin sayar da su lokacin da mutane ke bukata sai watan azumi tamkar haram ne. Shi yasa , inji shi kasuwani ke konewa ba zato ba tsammani.
A wasu kasuwanni da wakilinmu ya zaga ya gamu da shugabannin 'yan kasuwa suna zagayawa domin su gani da idanunsu yadda farashen kaya ke tashi.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.