Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararre A MDD Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Laifin Kisan Kiyashi Da Ake Zargin Iran Ta Aikata


Javaid Rehman
Javaid Rehman

A jiya Litinin Wani kwararre a Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a gudanar da binciken kasa da kasa kan "laifin cin zarafi da zalunci," da suka hada da kisan kiyashi kan 'yan tsiraru addinai da kuma kisan kare dangi ga 'yan adawa a shekarar 1980 da aka aikata a Iran.

Javaid Rehman, wakili na musamman mai zaman kansa kan halin da ake ciki a Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ya kamata a hukunta irin wannan babban take hakkin dan Adam, duk da la’akari da lokacin da aka aikata laifin.

Ya kara da cewa, "Kada a bar gwamnatin Iran da shugabanninta su kubuta daga laifukan da suka aikata na cin zarafin bil'adama da kisan kare dangi a kasar."

Yace, Wasu sun bada rahotan cewa, an yi wa mata fyade kafin a kashe su, kuma akwai yara da dama a cikin wadanda aka kashe.

zaben wakilan majalisar dokokin Iran.
zaben wakilan majalisar dokokin Iran.

Rehman ya koka da cewa, "An ci gaba da kai hari da cin zarafin 'yan tsiraru na addini, kabilanci da harshe da kuma 'yan adawa na siyasa ba tare da wani hukunci ba a tsawon shekaru goma na farko na kafa Jamhuriyar Musulunci a shekara ta 1979."

Ya yi tsokaci kan hare-haren da ake kaiwa Bahai - mafi yawan marasa rinjaye na Iran - wadanda ba musulmi ba - wanda ya ce "an yi ne da nufin kisan kare dangi da kuma zalunci."

Ba kamar sauran tsiraru ba, kundin tsarin mulkin Iran bai amince da addinin Bahais ba kuma ba su da wakilci a Majalisar dokoki.

Rehman, wanda Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta nada amma ba da yawun Majalisar Dinkin Duniya ya ke magana ba, ya yi nuni da rahotannin cewa, an kashe mabiya addini Bahais fiye da 200 daga farkon shekarun 1980, yayin da aka kama dubbai.

A yayin da Iran ke murkushe kungiyoyin da ke adawa da Musulunci, ya kuma bayar da shawarar cewa, su ma an yi wa masu bin tafarkin Markisanci da zindiqai da sauran mabiya wadansu addinai kisan kiyashi.

Javaid Rehman yana gabatar da rahoto gaban Hukumar kare hakkin bil'adama.
Javaid Rehman yana gabatar da rahoto gaban Hukumar kare hakkin bil'adama.

Rahoton na Rehman ya kuma yi nuni da kisan gillar da ake yi wa dubban matasa musamman matasa a gidajen yarin Iran a cikin 'yan watanni a lokacin bazara na shekara ta 1988, a daidai lokacin da ake kawo karshen yakin Iran da Iraki, yana mai bayyana hakan a matsayin "labari mai ban tsoro na ta'addanci."

Wadanda aka kashe galibi magoya bayan kungiyar Mujahedin ta Iran ne - kungiyar da Iran ta dauka a matsayin kungiyar ta'addanci da ke goyon bayan Bagadaza a lokacin rikicin.

Masanin ya koka da cewa "gwamnatin Iran tana ci gaba da musanta " aikata laifin ta'addanci," kuma ba a gurfanar da masu aikata laifin gaban kotu ba. Yace "samar da tsarin bincike na kasa da kasa mai zaman kansa a kan Iran yana da matukar muhimmanci."

Hukumar kare hakkin bil'adama a Geneva
Hukumar kare hakkin bil'adama a Geneva

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi gargadi a baya a cikin watan Afrilu cewa, cin zarafin da hukumomin Iran ke yi wa tsirarun ‘yan Bahai na take hakkin bil'adama ne

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG