Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tsaron Jihar Adamawa Yayi Taron Gaggawa Kan Wasu Tashintashina


kwamitin tsaron jihar Adamawa
kwamitin tsaron jihar Adamawa

Kwamitin tsaro na jihar Adamawa wanda ya kunshi manyan jami’an hukumomin tsaro na kasa, sarakuna da shugabannin addini sun yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da ake samu tsakanin fulani makiyaya da manoma tare da yin alwashin daukar tsauraran matakan tsaro baya tashin taron zaman gaggawa a fadar gwamnatin jiha.

Wannan taron na zuwa ne bayan tashe-tashen hankula a kananan hukumomi uku a kasa da mako guda wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka tara ciki harda ‘yan sandan kwantar da tarzoma hudu yayind aka sanar da bacewar waasu biyu da kuma lalata dukiyoyi da anfanin gona.

Bayanin bayan taro da kwamishinan yada labarai na jihar Aihaji Ahmed Sajo ya yiwa manema labarai ya ce daga yanzu wajibi ne shugabannin kananan hukumomi su rika taron tuntubar juna kan harkokin tsaro kowane mako kuma suna sanar da gwamna kan matsayin harkar tsaro a yankunansu.

Wakilin Muryar Amurka ya tambayi kwamshinan ko taron ya yi la’akari da yawaitar muggan makamai a hannun jama’a wanda sau tari suke anfani da su duk lokacin da aka sami rashi fahimtar juna , amma ya ce ba zai bayyana irin matakai ko dabarun da za su yi anfani da su wajen shawo kan tashe-tashe hankulan ba.

Kan batun ‘yansandan kwatar da tarzoma biyu da aka sanar da bacewarsu, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Malam Musa Kimo amma ya ki yace komi.

XS
SM
MD
LG