Rahotanni daga yankin na Karo da juna na wadanda suka yi nasarar dakile yunkurin harin kunar bakin waken sakanin 'yan banga da dakaran sojan rundunar ta ashirin da uku na garin Mubi.
Da yake bayanin afkuwar lamarin, shugaban karamar hukumar Madagali Alh. Yusuf Mohammed ya bukaci hukumomin tsaro su aike da karin jami'an tsaro saboda kusantar yankin da Sambisa. Yana Mai tabbacin 'yan banga ne suka tarwasa 'yan kunar bakin waken.
A daya bangaren kuwa, inji kakakin rundunar soja na ashirin da uku dake Mubi Manjo Akintola Badare ya ce dakarunsa sun shawo kan lamarin kuma hankula sun kwanta a yankin.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda ta jihar Adamawa DSP Othman Abubakar ya shaidawa yan jaridu cewa baya ga matan nan uku da aka tarwasa babu asarar rai ko raunuka.