A yayin da ake ci gaba da yabawa dakarun Najeriya game da nasarar da suka sami a dajin Sambisa,yanzu haka Gwamnoni da kuma Sarakunan gargajiya na gargadin al’ummomin da suka koma da a kula sakamakon rahotannin da ke cewa ‘yan Boko Haram, sun fantsama cikin al’umma.
Gwamnan jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da rikicin Boko Haram, yafi shafa, shi yayi wannan kira yayin kammala gasar karatun Al-Qur’ani da aka gudanar a yankin Mubi,da a baya ya fada hannun mayakan Boko Haram.
A bana wannan gasar shine na 31, a jihar Adamawa inda aka gudanar da gasar a garin Mubi, a wani yunkuri na tabbatar da cewa yanzu hankula sun kwanta a yankin da a baya ya zama cibiyar mulkin ‘yan Boko Haram, a arewacin jihar Adamawan,wato ‘’Madinatul Islam.’’
Yayin rufe gasar karatun alkur’anin mai martaba Sarkin Mubi,Lamido Abubakar Isa Ahmadu,ya ma alakanta rashin aikin yi da tumasanci da zama kandagarkin matsalolin da Najeriya ke fama da su batun da yace dole a tashi tsaye.
Shi ko Adamu Ahmad Umar dake zama shugaban kwamitin shirya gasar karatun yace sun shirya gasar ne don zaburar da dalibai sanin hakikanin karantarwar addini ba wai don cin mota da gida ba.
Tun farko a jawabinsa gwamnan jihar Adamawa Sen.Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla wanda kwamishinan harkokin yada labarai da tsare tsare,Ahmad Sajo ya wakilta,gwamnan yace abun farin ciki ne da a bana aka gudanar da gasar a yankin Mubi,to amma kuwa ya shawarci al’ummomin da suka koma yankunan su,da su kula,kasancewar yanzu akwai rahotannin cewa mayakan Boko Haram da suka gudo daga dajin sambisa sun fantsama cikin al’umma.
An dai gudanar da addu’u’oin na musamman da kuma karatukan alkur’ani mai tsarki don samun zaman lafiya.