Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Tantance Wadanda Rikicin Mambila Ya Rutsa Da Su Ya Mika Rahotonsa


 Kwamitin tantance sunayen wadanda aka kashe a rikicin Mambila
Kwamitin tantance sunayen wadanda aka kashe a rikicin Mambila

Watanni bayan tashe tashen hankulan da aka yi a yankin Mambilla na jihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da dama, kwamitin bincike da gwamnatin jihar ta kafa ya kammala aikin tantance sunayen wadanda aka kashe da gidajen da aka yi asara.

A karo na biyu kwamitin binciken gano adaddin asarar rayuka da kuma dukiyar da aka yi a yankin Mambilla sakamakon tashe tashen hankulan da aka yi a watannin baya da gwamnatin jihar Taraba ta kafa, ya kammala zamansa a Gembu na karamar hukumar Sardauna.

A wannan karon kwamitin ya tantance sunayen magada ne domin samun alkalumman wadanda aka kashe domin samun tallafi daga gwamnatin jihar.

Ambassada Emmanuel Njuwa shine shugaban wannan kwamitin. Yace sun hada rahotonsu kuma sun mikawa gwamnan jihar wanda zai yanke shawara akan irin taimakon da zai bayar

Wani mutum mai suna Bello wanda aka kashe dan’uwansa yace an dauki sunayen su, tare da alkawarin cewa gwamnati zata taimaka. Ita m wata mace mai Amina Saidu wanda mijinta lauya ne da aka kashe a rikicin Anguroji dake tsaunin Mambila ta ce ya barta da ‘ya’ya shida tayi farin ciki da taimakon da gwamnati zata bata.

Alhaji Umaru Zubairu, wakilin Mambila, ya ce abun da gwamnati ta yi abun godiya ne.

To sai dai kuma wasu na ganin akwai abun dubawa. Alhaji Bakari Muhammad Tamniya wani dan asalin yankin Mambila ya bada shawarar cewa kafa kwamiti yayi daidai, amma da wakilan kwamitin su kasance wasu daga wurare daban ne.

Yayin da kwamitin ke kammala aikinsa, wata sabuwa kuma ta kunno a yankin Yorro inda jami’an tsaro ke binciken kisan gillar da wasu matasan Mummuye suka yiwa wasu Fulani shida, batun da masarautar Mummuye dake tutiyar samun zaman lafiya ke cewa dole a yi bincike, domin hukunta mai laifi.

Saurari Rahoton Ibrahim Abdulaziz don jin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG