Babban darektan Hukumar Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Kasa ta Najeriya, Dr. Ado Mohammed, ya ce sun mike haikan a yanzu domin gudanar da rigakafi babu kaukautawa har sai an ga bayan wannan kwayar cuta daga Najeriya. Yace ya zuwa yanzu a bana, kananan hukumomi 12 ne kawai aka samu bullar wannan cuta cikinsu a jihohi guda 8. Wannan yana nufin cewa ba a samu rahoton wannan cuta a cikin jihohi 28 ba.
Yace shugaba Goodluck Jonathan ya gana da gwamnonin jihohin da abin ya shafa kuma har an fara ganin amfanin mikewar da suka kara yi wajen yakar cutar.
Dr. Ado Mohammed, yana magana ne a fadar Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammadu Sunusi.
Yace a cikin watanni 7 da suka shige, ba a samu rahoton bullar kwayar cutar shan inna ko sau daya a cikin jihar Jigawa ba, yana mai fadin cewa a fadin Najeriya ma baki daya, san samu raguwar cutar da kashi 70 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar da ta shige ta 2012.
Sarkin Dutse dai yace bai yi mamakin irin nasarar da aka samu a Jihar Jigawa ba a saboda yadda gwamnatin jihar ta kuduri aniyar ganin bayan wannan cuta.