Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bauchi: Jam'iyyar PDP Ta Kalubalanci Digirin-Digirgir Da Jami'ar Cotonou Ta Ba Gwamnan Jihar


Jam’iyyar PDP a jihar Bauchi ta kalubalanci sahihancin digirin-digirgir da wata jami’ar kasar waje ta baiwa gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar.

A ranar talatin ga watan satumbar wannan shekara ne dai jami’ar Estam dake Cotonou a jamhuriyar Benin ta baiwa gwamnan digirin-digirgir a matsayin wanda yayi zarra a fannin salon mulki a fadin Nahiyar Afrika,

A tattanawa da manema labarai kan batun, jigon jam’iyyar PDP a jihar ta Bauchi, Alhaji Salihu Ya’u Nabaddo, ya bayyana shakkar sa a cewa gwamnan jihar shine yayi fice a salon mulki a fadin Nahiyar Afirka, kamar yadda yabayyana dalilansa na cewa mai yasa duk jami’oin dake fadin Najeriya basu ga kwarewar gwamnan ba sai wata jami’a dake Cotonou! Dan haka a cewar sa bai dace ba sam.

A nata ba’asin, jam’iyya mai mulki APC, ta bakin jami’in hulda da jama’a Alhaji Auwal Jalla, ya bayyana irin ayyukan da gwamnan ya aiwatar da suka sa wannan jami’a ta bashi wannan takardar karramawa ta digirin digirgir.

Domin Karin bayani, saurari rahoton Abdulwahab Muhammed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG