Kwamitin zai duba hanyoyin da za’a karfafa zamantakewar jama’ar kasashen biyu da bunkasa harkokin kasuwanci da zummar taimakawa tattalin arzikinsu.
Haka kuma kwamitin zai dinga lura da shige da ficen baki saboda dakile duk wata matsalar tsaro da ka iya tasowa akan iyakokinsu.
Karamar Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim tace kafa kwamitin shi ne matakin farko na cimma manufofin da kasashen biyu suka saka a gabansu. Ministar tace Najeriya da Nijar tamkar kasa daya ne, har ta kara da cewa “mun fi kusa dasu, sun fi kusa damu”.
A cewar minister nan gaba za’a kafa irin wannan kwamitin na bunkasa harakokin kasuwanci da zumunci tsakanin Najeriya da sauran makwaftanta kamar Kamaru da Chadi, don, a cewarta, ya kamata a sami irin haka a tsakanin dukkan kasashen dake cikin Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma taECOWAS.
Da yake bayyanawa wakiliyarmu Medina Dauna irin hanyoyin da zasu bi domin aiwatar da aikin,Shugaban kwamitin kuma babban darakta a hukumar dake kula da kan iyakokin Najeriya Muhammad Bosa Ahmed yace akwai bukatar a fara tunashe da jama’ar kasashen Najeriya da Nijar cewa kodayake turawa sun raba kasashen biyu amma a akasarin gaskiya al’umma daya ce.
Wakiliyar Jamhuriyar Nijar a wajen hidimar, Jakadiya Amina Jibrila Maiga ce suna fatan shugabannin kasashen biyu zasu ciwo kan matsalolin da ake fuskanta domin kasuwanci ya samu ya bunkasa.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Facebook Forum