Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamandan Mayakan Boko Haram Da Wasu Mutum 5 Sun Mika Wuya Ga Sojoji A Borno


Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa

Masu tada kayar bayan sun yi watsi da ayyukan ta'addanci tare da mika wuya ga sojojin ne a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki.

Mayakan Boko Haram 6 ciki harda kwamandan 'yan ta’adda sun mika wuya ga dakarun Rundunar MNJTF, ta hadin gwiwar kasa da kasa.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, babban jami'in yada labaran rundunar ta MNJTF, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya bayyana sunan kwamandan 'yan taaddar da Adamu Muhammad.

Ya kuma zayyano sunayen sauran 'yan taaddar da Isah Ali mai shekaru 18 da Hassan Modu dan shekara 18 da Nasir Idris mai shekaru 23 dogarin kwamanda Jubilaram, Usman Rash da Abba Aji mai shekaru 21 da kuma Abubakar Isah dan shekara 20.

A cewar sanarwar, "'yan ta’addar sun tsere daga maboyar tsagin ISWAP dake Jubilaram, dake shiyar kudancin tafkin Chadi.

Adamu mai shekaru 22, ya taka rawa a hare-hare da dama da aka kai kuma ya karade garuruwan Kangarwa da Alagarno da Doro Naira da Dogon Chikwu dake karamar hukumar kukawa ta jihar Borno".

A cewar kakakin Rundunar ta MNJTF, fiye da 'yan taadda 100 ne suka tuba tun bayan da aka kaddamar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsaftace yankin tafkin Chadi mai lakabin "Operation Lake Sanity" a turance wanda manufarsa itace kakabe masu tada kayar baya daga yankin.

Yace tun daga ranar 23 ga watan afrilun daya gabata, masu tada kayar baya 119 ne suka mika wuya tare da yin kira ga takwarorinsu su rungumi tafarkin zaman lafiya tare da ajiye makamai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG