Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Mata A Abuja Sun Yi Zanga Zanga Kan Yin Watsi Da Bukatun Kara Musu Kaso A Manyan Mukaman Siyasa


Majalisar Dokokin Najeriya (Twitter/National Assembly)
Majalisar Dokokin Najeriya (Twitter/National Assembly)

Kasa da sa’o’i 24 da Majalisun tarayyar Najeriya suka yi watsi da kudurin da ke nemawa mata kari na kaso 35 cikin 100 na muhimman mukamai musamman na siyasa a kasar, daruruwan mata a karkashin inuwar kungiyoyi da dama suka fito zanga zangar lumana domin nuna bacin ransu game da matakin Majalisun.

ABUJA, NAJERIYA - Daruruwan mata a karkashin kungiyoyi kamar su Action Aid, da WRAPA mai nema wa mata 'yancinsu, da kungiyar WIMBIZ mai taimaka wa mata masu sana’a da dai sauransu ne suka fito zanga zangar lumanar domin neman ‘yan Majalisar dokokin Najeriya su sake nazari akan matakan da suka dauka na yin watsi da kudurin ba mata damar shiga cikin sha’anin tafiyar da kasa, suna mai cewa ba su san inda aka sami matsala ba saboda tun farko mazan sun nuna musu goyon baya dari bisa dari.

Ene Obi, da ke zaman babbar wakiliya a kungiyar Action Aid a Najeriya, ta bayyana cewa ya zama wajibi ‘yan Majalisar su sake nazari su zartar da kudurin ya zama doka don ba mata damar wakilcin da ya kamata.

‘Yar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isuikwato/Ummunneochi, Nkiruka Onyejocha, ta fito rarrashin ‘yan uwanta mata da su yi hakuri su koma gida a daura damarar sake nazari don fito da sabbin dabarun da zasu taimaka wajen shawo kan maza su ba su hakkinsu.

Ita ma tsohuwar ministar ayyukan mata Malama Aisha Isma’il ta bayyana rashin jin dadinta kan wannan batu.

A ranar Talata ne dai Majalisar dokokin Najeriya ta yi watsi da kudurin nema wa mata kaso 35 a bangaren samun mukaman siyasa don su taimaka wa ‘yan uwansu da kuma neman ci gaban kasa.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG