Kungiyoyar likitoci masu aiki a asibitocin gwamnati a Najeriya ta tsunduma yajin aiki a yau Litinin saboda rashin samun isassun kayayyakin kariya da kuma kudade a yayin da ake fama da cutar Coronavirus.
Those treating COVID-19 patients will stay on the job but their union, the National Association of Resident Doctors (NARD), gave the government two weeks to meet the demands or else they would also walk out.
Wadanda ke kula da masu dauke da cutar Coronavirus za su ci gaba da aiki amma kungiyarsu ta likitocin 'yan cikin gida masu neman kwarewa da ke aiki a asibitocin gwamnati (NARD) ta baiwa gwamnati wa'adin mako biyu ta biya musu bukatunsu ko kuma su shiga yajin aikin su ma.
Likitoci masu neman kwarewa su ne wadanda suka kammala makarantar koyon aikin likita kuma suke aiki domin zama kwararru.
Suna da matukar muhimmanci a Najeriya, duba da yadda suka cika bangarorin kulawar gaggawa da ke cikin asibitoci a kasar.
A cikin wata sanarwa shugaban kungiyar Aliyu Sokomba ya ce "Idan gwamnati ba ta ba mu abin da mu ke bukata nan da mako 2 ba, to duk wani likitanmu da ke aiki a cibiyoyin da aka ware domin kula da masu cutar Coronavirus su ma za su fara yajin aiki."
Likitocin na neman a ba su karin kudade yayin wannan annoba ta Coronavirus, su na kuma neman a ba su inshorar rayuwa da kuma karin a kudaden samun kwarewa da sauran bukatu.
Kungiyar ta kuma yi korafin rashin kayan kariya domin kula da masu cutar Coronavirus. A cewar ta, likitocin sun soma sun rasa rayukansu bayan da su ka Kamu da wanna cutar ta Covid-19.
Najeriya na da fiye da mutum 16,000 masu dauke da cutar Coronavirus, yayin da mutum 420 Suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
Facebook Forum