A Najeriya yajin aikin da likitocin kasar suka shiga kan batun neman alawus-alawus da kayyakin kariya na aikin asibiti ga likitoci da ke kan gaba a yaki da cutar COVID-19 a kasar ya shiga yini na hudu.
Kungiyar likitocin kasar ta gargadi gwamnati akan biyan hakokin ma’aikatanta ko kuma ta shiga yajin aiki na gama-gari .
Sai dai duk da hakan gwamnati ta yi kunnen kashi inda ta ce sai an bi matakai kafin akai ga cimma dukkan bukatuntu lamarin da ya janyo ake cikin yini na hudu da soma yajin aiki na manyan likitoci a kasar.
Wani majinyaci mai suna Hamisu Abubakar a asibitin Garki da ke babban binrin tarayyar kasar ya ce ya shiga mummunan hali sakamakon zuwa asibiti bai tarar da likitan da zai duba shi ba.
Dr. Hassan Ibrahim na Asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya ce yajin aiki na manya likitoci a kasar na da matukar hatsari duba da irin gudumawarsu da suke bayarwa ga fanni lafiya.
Bayan taron da gwamnatin kasar ta yi da shugabannin kungiyar likitocin a ranar Talata wanda aka tashi ba tare da cimma wata mafita ba, Shugaban Kungiyar Aliyu Sokombo ya bayyana cewa sai da suka bi matakai kafin akai ga cimma wannan matsaya na shiga yajin aikin.
Ya kara kira ga gwamnati da ta biya likitoci albashinsu da ba’a biya a baya ba da alawus-alawus na aikin kariya daga daukar cututtuka masu yaduwa da kuma samar musu da wadatattun kayayyakin aiki na asibiti.
Ministan kiwon lafiya Mr Osagie Ehanire ya ce bukatun da likitocin suka gabatar a wannan lokaci da kasar ke fama da annobar cutar coronavirus ka iya sa a rasa rayukan al’umma inda ya yi kira a gare su da su tausaya.
Ma’aikatan lafiya dai suke kan gaba wajen duba majinyata da ke dauke da cututtuka masu hadari da kuma yaduwa kamar cutar COVID-19 da ke sarke numfashi.
Saurara karin bayani a sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Facebook Forum