Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin ISIS da al-Shabab Suna Bata Addinin Musulunci


Mayakan ISIS suna hallaka wasu
Mayakan ISIS suna hallaka wasu

Babban limamin masallacin Minneapolis dake Amurka Shaikh Abdirahman Omar yace kungiyar ISIS ta hallaka duk malaman addinin Islama da masana da dimbin musulmai duk da cewa wai tana kare musulunci ne.

Babu shakka yadda 'yan kungiyar ISIS da ta kafa Daular Islama ke gudanar da abubuwanta ya damu wasu musulman duniya. Irin wannan tunanen yasa limamin masallacin birnin Minneapolis dake jihar Minesota a kasar Amurka ya yi tur da kakkausan lafazi da take taken kungiyar ISIS.

Sheikh Abdirahman Omar limamin masallacin ya damu da yadda kungiyar ke garkuwa da mutane kana daga baya ta sare kawunansu duk da sunan addinin musulunci. Yayin da yake magana da Muryar Amurka sashen Somali yace bisa ga tsarin shari'ar musulunci wadanda aka kama lokacin yaki suna da 'yanci. Ban da haka shari'ar musulunci bata yadda a kashe wani ba sabili da kasar da ya fito. Yin hakan ba komi ba ne illa jahilci da kuma shafawa addinin Musulunci kashin kaza.

Sheikh Omar yana ganin kungiyar ISIS da al-Shabab tamkar Danjuma da Danjummai ne, wato jirgi daya ya kawosu, akidarsu daya, tafiyarsu daya domin abubuwan da su keyi suna bata addinin musulunci ne kawai. Maimakon su jawo mutane su shiga addinin, halayensu na bakanta addinin gaban mutane. Ba zata yiwu ba wasu su ji sha'awar shiga addinin.

Yace a duba wadanda suke ikirarin kafa Daular Islama sun kashe duk shehunan addinin wadanda suke koyas da mutane su kuma fadakar dasu.Duk wani masani da yayi fice sun kashe. Hatta ma cikin masallatai sun bi limamai sun kashe. Sun kashe mutane masu dimbin yawa wadanda ba'a san iyakarsu ba. Mutanen da suka kashe basu ci ba basu sha ba. Duk da barnar da su keyi suna ikirarin wai suna ceto mutanen ne. Babu wanda ya tsira a hannunsu har da ma musulman. Kididigar wadanda suka kashe ya nuna cewa a akasarin gaskiya me sun kashe musulmai fiye da kowa.

Sheikh Omar y ce akwai bukatar jami'an gwamnatin Amurka su kara yin kokarin nunawa duniya cewa ba da addinin Islama kasar ke yaki ba.

Sheikh Omar ya kara jaddada irin karan tsanar da ake dorawa Musulmi a Amurka tun bayan hare-haren ta'addancin ranar 11 ga watan 9 na shekarar 2001. Akwai wasu rukunin musulmai wadanda aka haramtawa tafiya ta jiragen sama. A jefi jefi akan yiwa musulmai tambayoyi masu tsanani da kuma ban tsoro game da rayuwar Musulmi. A fili take cewa a nan Amurka an zurawa Musulmai ido. Ana sa ido a Masallatai tare da satar sauraron maganganun Musulmi da suke yi a tarho ko irin sakonnin da suke aikawa.

Yadda ake yada labarin wasu 'yan Amurka da suke sulalewa zuwa shiga kungiyar ISIS ko al-Shabab mahukuntan kasar na zaton da hannun al'ummar Musulmin Amurka lamarin da yasa wasu sun dauka kasar ma na yaki da Musulmai ne. Alhali kuwa mun san ba da Musulmi Amurka ke yaki ba. Wannan rudanin yasa ana samun karuwar masu zuwa suna taya masu tsattsauran ra'ayi yaki a faggen daga.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG