Jiragen yakin Amurka sun kai hare hare kan cibiyoyin kungiyar ISIS a kudu maso yammacin Bagadaza, a wani matakin fadada kamfen da Amurka take dauka kan kungiyar mayakan sakan a Iraqi.
Ma’aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon ta a fada daren jiya litinin cewa wannan shine farmaki na farko a banagaren fadada hare hare da Amurka take kaiwa wanda ya wuce burin kare jami’ai da muradunta, yayinda ita kungiyar ta ISIS ma take kai farmaki.
Haka kuma Amurka ta kai wani farmaki da jiragen yaki kusa da tsaunukan da ake kira Sinjar a arewacin Iraqi.
A makon jiya ne shugaban Amurka Barack Obama ya gayawa Amurkawa cewa hukumomin kasar zasu fadada matakan soji da take dauka kan kungiyar ISIL a wani yunkurin da babu kakkautawa na ganin bayan mayakan sakan ko da kuwa a ina suke.
Mr. Obama ya bada umarnin a kai farmaki kan kungiyar ISIS a Syria, amma har yanzu bai yanke shawarar fara kai irin wadannan hare hare ba.
Wani babban jami’in Amurka ya gargadi Syria cewa kada tayi katsalandan da matakan sojin da Amurka zata dauka ta sama, domin Washington zata iya maida martini ta wajen kai hare hare kan cibiyoyin tsaron kasar.