Yau Laraba da maraice ne shugaban Amurka Barack Obama zai yi jawabi ta talabijin ga Amurkawa inda ake sa ran zai bayyana shirin gwamnatinsa na yaki da masu tsatsauran ra’ayin Islama na kungiyar ISIS.
Kakakin fadar white House Josh Earnest yace Mr. Obama ya hakikance cewa wannan batu yana da muhimmancin matuka ga tsaron Amurka.
Kakakin ya kara da cewa shugaban na Amurka zaiyi magana kan irin barazanar da mayakan sakan suke haddasawa da kuma shirinsa na warga kungiyar.
Ernest bai bayyana dalla dalla abun da Mr. Obama zai fada ba. Amma shugaban na Amurka yace Amurka ba zata sake tura sojojinta zuwa Iraqi ba.
Jiya Talata shugaban na Amurka ya gana da shugabannin majalisun dokokin Amurka ‘yan Democrat da na Repulican kan shirye shiryen da yake yi gameda ISIS.
Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka sun dage cewa shugaban ya nemi amincear majalisa kamin ya dauki kowane irin matakin soja kan kungiyar ISIS harda ma kai farmaki ta sama a Syria.
Amma fadar white House tace Mr. Obama ya gayawa shugabannin majalisun dokokin Amurka cewa yana da ikon daukan kowane irin mataki ba tareda ya nemi yardarsu ba tukunna.