Har yanzu kan batun yaki da kungiyar ISIS, Iran tace taki ta amincewa da bukatar da Amurka ta gabatar mata na neman ta shiga sahun kasashe da suke yaki da kungiyar mayakan sakan a Iraqi.
A kalamai da yayi a tashar talabijin ta kasar, shugaban addini a Iran, Ayatollah Ali khameni, yace jakadan Amurka a Iraqi ne nemi hadin kan Iran, amma tayi watsi da bukatar sabo da acewarsa “hannayen Amurka suna da dauda.”.
Ayatollahi yace kalaman Amurka na kaddamar rundunar taron dangi domin a yaki da kungiyar ISIL coge ne kawai kuma tana yi ne da son zuciya.
Jiya litinin Amurka tace sam ba zata hada kai ta fuskar soji da Iran wajen yaki da mayakan sakan ISIS a Iraqi ba, amma tace ba zai hana nan gaba ta tattauna da kasar kan batu idan bukatar haka ta taso.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, tace ai ba sirri bane cewa Amurka ta tattauna da Iran kan girka rundunar taron dangi domin yaki da kungiyar ISIS a Iraqi. Duk da haka tace “jami’an Amurka ba zasu yi aiki tare da Iran ta fuskar soji a yaki da Amurkan take yi da masu tsatsatsauran ra’ayin ba.
A cikin wata rubutacciyar sanarwa data bayar, Psaki tace kungiyar ISIS tana mummunar barazana ga Iran kamar yadda take barazana ga wasu kasashe da suke yankin”.