Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

#ENDSARS: Kungiyoyin Addinai Da Al’umma Sun Yi Gargadi


Gwamnan Jihar Pilato, Samuel Lalong (Hoto: Twitter @PLSGov)
Gwamnan Jihar Pilato, Samuel Lalong (Hoto: Twitter @PLSGov)

Biyo bayan zanga zangar #ENDSARS data rikide ta zama tashin hankali, matasa suka shiga wawashe rumbunan ajiyan kayan abinci na gwamnati da kwashe wasu kayan aiki a ofisoshin gwamnati, shugabannan al’umma da na addinai sunyi huduba ga matasan da su kasance nagari.

Shugaban kungiyar hadin kan kirista wato CAN, reshen jahar Pilato, Rabaran Fada Polycap Lubo yace, ya kamata matasan su baiwa gwamnati damar duba bukatun da suka gabatar mata.

Mai martaba Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna, yace, tilas ne hukumomi su zauna da masu tada hankalin don samun masalaha.

Komishinan yada labarai da sadarwa a jahar Pilato, Dan Manjang, a nasa bangaren ya yi kira ga jama’a da su yi hakuri da juna domin samun dawwamamman zaman lafiya.

Rundunar tsaro ta STF a jahar Pilato, ita kuma tace ta kame mutane fiye da dari uku da ake zarginsu da fasa rumbuna, ofisoshin gwamnati da gidajen wasu mutane a jihar da zimmar kwashe musu kadarori a matsayin ganima.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti:

Anyway Matasa Gargadi Kan Warwason Kayan Abinci A Filato
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG