Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata A Bai Wa 'Yan Jarida Kariya A Najeriya - Gwamnan Kogi


Gwamna Yahaya Bello a lokacin bikin tunawa da mazan jiya a watan Janairu 2021 (Instagram/officialgybkogi)
Gwamna Yahaya Bello a lokacin bikin tunawa da mazan jiya a watan Janairu 2021 (Instagram/officialgybkogi)

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bukaci rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da cikakken bincike kan mutuwar dan jaridar Vanguard, Henry Tordue Salem wanda aka gano gawarsa a asibitin gwamnati na Wuse a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Bello ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Onogwu Muhammed ya fitar inda ya jajanta wa iyalan marigayi dan jaridan, kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya wato NUJ da kuma kungiyar ‘yan jarida ta majalisar wakilai kan babban rashin.

Yahaya Bello ya kuma bayyana bakin cikinsa kan rasuwar dan jaridan, inda ya ce akwai shakku kan al’amuran da suka shafi mutuwarsa.

A cewarsa, ‘yan jarida a Najeriya sun cancanci a basu cikakken kariya la’akari da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen fadakar da jama’a tare da sa ido kan ayyukan gwamnati.

Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro da su kara zage damtse wajen samar da isasshen tsaro ga ‘yan kasar, kana kuma ya yi addu’ar Allah ya ba wa iyalan marigayin hakurin jure rashinsa.

An dai tsinci gawar dan jarida Henry Tordue Salem da ya bata tun ranar 13 ga watan Oktoba, a dakin ajiye gawa na babban asibitin gwamnati dake Wuse a ranar 12 ga watan Nuwamba.

Marigayi dan jaridan Vanguar Henry Tordue Salem.
Marigayi dan jaridan Vanguar Henry Tordue Salem.

A ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba ma sai da ‘yan jarida suka mamaye hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja domin nuna rashin jin dadinsu kan ci gaba da bacewar Salem, kuma suka bukaci ‘yan sanda da DSS su taimaka wajen neman inda marigayin dan jaridan ya shiga.

'Yan jaridan da suka gudanar da zanga-zanga a kan bacewar marigayi Henry Tordue Salem.
'Yan jaridan da suka gudanar da zanga-zanga a kan bacewar marigayi Henry Tordue Salem.

A yayin zanga-zangar, jami’in hulda da jama’a na hedikwatar ‘yan sanda, Frank Mba, ya yi jawabi ga jama’a, inda ya ce ana ci gaba da kokarin gano inda Salem ya shiga kafin daga baya aka gano gawaras a dakin ajiye gawa na asibitin Wuse.

'Yan jaridan da suka gudanar da zanga-zanga a kan bacewar marigayi Henry Tordue Salem.
'Yan jaridan da suka gudanar da zanga-zanga a kan bacewar marigayi Henry Tordue Salem.

Daga baya rundunar 'yan sanda ta kama wani direba mai suna Itoro Clement da ake zargin ya buge dan jaridar Salem har lahira.

A lokacin wata ganawa da manema labarai, kakakin rundunar 'yan sanda Frank Mba ya bayyana cewa an kama direban ne a ranar Juma’a a Abuja, sakamakon wani bincike da sashen binciken rundunar ya gudanar.

Clement Itoro direben da ake zargin ya amince cewa ya buge wani mai tafiya a kasa da bai san ko wanene shi ba a unguwar Mabushi da misalin karfe 10 na dare a ranar da Tordue Salem ya bace.

Sai dai ya ce bai tsaya wurin da hatsarin ya auku ba saboda yana tsoron kada ya kasance ‘yan fashi da makami da ke addabar mutane a unguwar ne ke neman kai masa hari.

Tuni dai yan uwan marigayi Salem suka yi ta yin kiran a kan gwamnati ta gudanar da bincike don gano wanda ya kashe dan uwan nasu.

Tun ba yau ba kuma 'yan jarida ke fafutukar neman kariya daga hukumomin tsaro domin yadda wasu ke shiga cikin hatsarin gaske, wasu lokuta ma ana barazana ga rayukansu a yayin gudanar da aiki.

XS
SM
MD
LG