Rundunar sojojin Najeriya ta ce za ta fara tafiya da ‘yan jarida fagen daga a yakin da ta ke da 'yan ta'addan Boko Haram a shiyar Arewa maso gabas.
Kakakin sojojin Najeriya Kanar Sagir Musa ya ce za a rika shiga da ‘yan jaridan ainihin wuraren da ake fafatawa don dauko labaran yaki.
Ya kuma ce an shirya tsaf domin kare lafiyarsu.
Daga ranar 6 ga watan Afrilun nan ne dai za a fara tafiya da ‘yan jaridan zuwa fagen daga.
Tuni dai uwar kungiyar ‘yan jaridun Najeriya wato NUJ ta yi na'am da wannan mataki kamar yadda sakatarenta, Shuaibu Usman Leman ke cewa “hakan zai taimaka a wannan yaki domin a samu gaya wa 'yan kasa gaskiyar yadda yakin ke tafiya.”
Sai dai kuma kungiyar ta NUJ ta nemi sojojin da su lura da 'yan jaridan a basu inshorar rayuwa a kuma kare su.
Tsohon babban kwamandan rundunar yaki da Boko Haram, Manjo Janar Junaidu Bindawa ya ce hikimar da ke tattare da kai ‘yan jaridan fagen daga shi ne zasu gane wa idonsu ainihin abin da ke faruwa su kuma sanar da jama'a.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum