Cikin kayan da hukumar kwastan ta kama akwai kwayoyin dake saka maye na Tramadol cikin manyan motoci biyu da tayoyin mota da daskararrun kaji da dai sauransu.
Sakamakon kamen da hukumar Kwastan mai kula da shiyyar Legas da Ogun ta yi, a karkashin jagorancin kwantirola Mohammed Uba Umar, hukumar ta cafke mutane 15 da ake zargi da shigar da kayayyakin da aka haramta shiga da su Najeriya, ko kuma aka yi kwangen biyan kudaden haraji ga gwamnatin taryyar Najeriya, wanda kudinsu ya kai sama da Naira Miliyan 200.
Da yake ‘karin haske game da wannan kame da hukumar ta yi, Kwantirola Mahammed Uba, ya tabbatar da cewa sun kama wasu tsofaffin tayoyin mota da suka kai adadin dubu biyar da goma sha hudu da gwamnatin ta haramta shigowa da su Najeriya, sai kuma shinkafa da itama gwamnati ta haramta shiga da ita ta kan iyakokin kasa.
Haka kuma an kama wasu na’urorin girki da ake kira risho, wadanda aka bayyana su da sunan wani abu na daban a rubuce, hakan yasa aka kwace kayan domin an sabawa doka. Sai kuma kayayyakin gwanjo da hukumar lafiya ta haramta shiga da su kasar.
Hukumar Kwastan ta kama ‘daya daga cikin manyan motocin kamfanin shahararren ‘dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote, dauke da daskararrun Kaji katon 1,200 wadanda suma aka haramta shiga da su.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum