Wannan rashin amincewar majalisar dattawa ya harzuka kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi shirin famtsamawa cikin wani yajin aiki na gama gari a duk fadin Najeriya. To amma sai gashi kungiyar ba zato ba tsammani ta janye shirin. Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya ya bi digdigin ya san ko menene ya kawo hakan.
Shugaban kungiyar ya ce kakakin majalisar wakilai shi ya rokesu kada su shiga yajin aiki ganin yadda maganarsu ta samu karbuwa a majalisarsu da kuma yadda majalisar ta yi la'akari da manufofin 'yan Najeriya. Ya ce kodayake a da can majalisar dattawa ta yi watsi da maganarsu wannan ba shi ba ne karshen kokarin yiwa kundun tsarin kasar kyaran fuska ba. Shugaban kungiyar ma'aikatan ya ce sabili da bayanin da kakakin majalisar ya bayar shi yasa suka gani yakamata su girmama majalisar, su dakata, su kuma jira har sai maganar ta kai gaban shugaban kasa ya sa hannu ta zama doka.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.