Wakilin sashen Hausa, Murtala Faruq Sanyinna, yace ya ga matasa 9 da suka ji rauni a asibitin cikin daren nan, yayin da wata majiya a asibitin ta shaida masa cewa matasa uku sun rasa rayukansu, kuma an ajiywe gawarwakinsu a dakin ajiye gawa na asibitin.
Sai dai kuma wata majiyar dabam ta hukuma mai nasaba da gidan gwamnatin Sokoto, ta ce babu wanda ya rasu a wannan lamarin.
Mazauna unguwar da gidan gwamnatin yake sun ce daruruwan matasa sun taru suka yi cincirindo su na jiran a rarraba musu kyautar kayan Sallah, sun kuma musanta cewa wani turken wutar lantarki ne ya fado ya haddasa gudu da tattake mutane a wurin.
Haka kuma sun ce ba wai rabon kayan buda-baki ne ya tara matasan a wurin kamar yadda aka yi ta fada tun da farko ba.
Har yanzu ba a ji wani labari daga bakin gwamnatin Jihar ta Sokoto kan wannan lamari da ya faru cikin daren nan ba.
Ga cikakken bayanin da Murtala Faruq Sanyinna yayi ma Ibrahim Ka-Almasih Garba a tattaunawarsu kan wannan batun dazu da asuba.