Jihar Katsina tamkar ta zama matattarar masu fasakwaurin miyagun kwayoyi. Hukumar kwastan ta Najeriya ta ce hakinta ne ta tabbatar cewa duk abun da dokar kasa ta hana a shigo da shi ita ma ta hana. Ya ce abun tsoro kuma abun takaici ne cewa duk wata kwaya mai sa maye yanzu ana shigo da ita ta hanyar Katsina. Daraktan kwastan Alhaji Nde ya ce hatta rumbun da suke ajiye kayan da suka kama ya cika da miyagun kwayoyi. Ya ce kamata yayi mutanen gari idan sun ga irin wadannan abubuwa su taimaka a hana. Kwayoyi masu sa maye zasu nakasa matasa su sa karfinsu ya kare, su lalace. Su basu yi karatu ba basu yi ma kansu anfani ba balantana su taimakawa cigaban kasa. Ya ce saboda haka idan aka bari miyagun kwayoyi suka cigaba da shigowa samarin jihar Katsina ne zasu tagayyara domin za'a kashe kwakwalwarsu, a kashe iliminsu da ma hallaka rayuwarsu gaba daya.
Hukumar kwastan ta kama mutane da dama har da ma wani da yayi kokarin bada cin hanci na nera miliyan biyar. Ana gurfanar da mutane gaban sharia. Alhaji Nde ya ce duk sati sai sun yi kamu a jihar ta Katsina. Ya ce babu wani wuri a Najeriya inda suke kama mutane game da miyagun kwayoyi idan ba Katsina ba. Idan sun kama mutane suna mika su ga hukumar dake yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA.
Dangane da matsalolin da suke fuskanta Alhaji Nde ya ambato uku masu mahimmanci. Na daya rashin samun hadin kai da mutanen jihar domin basu fahimta da abun dake faruwa ba ko illar dake tafe da miyagun kwayoyi. Abu na biyu shi ne kasashen dake makwaftaka da Najeriya basu damu ba domin ba a kasashensu a ke anfani da kwayoyin ba. Abu na uku kuma na karshe shi ne rashin yin hukunci cikin gaggawa kuma mai tsanani. Ya ce domin duk wanda ya ke fataucin miyagun kwayoyi da zai tagayyara mutane to shi ma abarshi ya lalace a gidan kaso.
Ga karin bayani.