Kungiyar kwallon Kafa ta Lyon, dake kasar faransa na fuskantar dakatar da gasar Turai bayan da hukumar kula da kwallon Kafa ta turai Uefa ta kalubalance ta akan taron jama'a da ya wuce adadi kafin wasansu na ranar Alhamis da CSKA Moscow a gasar Europa League, inda aka doke kungiyar ta Lyon, da ci 3-2 wanda hakan yayi sanadiyyar cire ta a gasar ta bana.
Har ila yau ana tuhumar Lyon, din da halayyar nuna wariyar launin fata, tashin hankali na jama'a, jifa da wasu kayan aiki da kuma kunna wuta a filin wasan da toshe hanyoyin shiga filin a ranar da ake wasan.
'Yan sanda sun ce sama da mutune 150' suka tasar wa jami'in tsaro a filin Lyon a ranar Alhamis. din da ta gabata.
Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce zata yi zama kan wannan batun don magance matsalar a ranar 31 ga Mayu, 2018.
Facebook Forum