Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Lauyoyin Gambia Ta Gabatarwa Najeriya Korafinta Akan Alkalin Alkalan Kasarsu


Shugaban Gambia Yahya Jammeh da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari a ganawar kawo sulhu a kasar
Shugaban Gambia Yahya Jammeh da Shugaban Najeriya Muhammad Buhari a ganawar kawo sulhu a kasar

Alkalin alkalan kasar Gambia Emmanuel Fagbule dan Najeriya ne kuma wai na hannun daman shugaba Yahya Jammeh ne saboda haka lauyoyin kasar ta Gambia suna ganin ba zai yi adalci a shari'ar da Yahya Jammehn ya shigar gabansa ba kan zaben makon jiya.

Baicin korafin cewa alkalin alkalan kasar Gambia Emmanuel Fagbule ba zai yi adalci ba a karar da shugaba Yahya Jammeh ya shigar, lauyoyin Gambia har wa yau suna korafi akan yadda mahukuntan Gambia suke hayar lauyoyi daga Najeriya din domin su kifar da sakamakon zaben makon jiya.

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya Barrister Mahmud ya tabbatar cewa sun samu korafin daga lauyoyin Gambia kuma zasu dauki matakan da suka dace domin tabbatar an yi abun da ya kamata, babu wanda ya cutu.

Tuni dai wasu lauyoyi a Najeriya suka fara fargaban yin adalci a shari'ar shugaba Yahya Jammeh a Gambia.

Barrister Yakubu Bawa Manufanshi lauyan tsarin mulki ne yace babu shakka akwai matsala. Yace ana iya a canza sakamakon a tabbatar da shi Yahya Jammeh saboda ya fi karfin kowa a karamar kasar.

Ambassador Yusuf Mamman yana ganin shiga tsakanin da shugabannin yammacin Afirka suka yi za'a cimma nasara domin shi Yahya Jammeh yana neman yadda zai fita ba tare da wulakanci ba ne.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG