Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar AU Ta Kalubalanci Jammeh Kan Sakamakon Zabe


Shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, Nkosazana Dlamini-Zuma, a lokacin wani taro a birnin Geneva na Switzerland
Shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, Nkosazana Dlamini-Zuma, a lokacin wani taro a birnin Geneva na Switzerland

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta yi kira ga shugaban Gambia Yahya Jammeh da ya amince da sakamakon zaben da aka yi a farkon watan nan, kamar yadda ya yi a baya.

Shugabar kungiyar, Nkosozana Dlamini-Zuma ta yi kira ga shugaba Jammeh da ya tabbatar ya mika mulki cikin kwanciyar hankali da lumana.

A ranar 1 ga watan Disamba, Jammeh ya amince da shan kaye a zaben, inda har ya kira abokin hamayyarsa Adama Barrow ta wayar talho ya taya shi murnar.

“Ina maka fatan Alheri, mulkin kasar nan zai koma hanunka a watan Janairu." In ji Jammeh jim kadan bayan an sanar da sakamakon zabe.

To sai dai a jiya Juma’a shugaba Jammeh ya ce akwai kurakurai a zaben “wadanda ba za a amince da su ba.”

Ya kara da cewa jami’an zabe ne su ka gano cewa an tafka kura-kuran, saboda haka ya na kalubalantar sakamakon zaben.

Amma kungiyar tarayyar ta Afirka ta ce, wannan amai da Jammeh ya yi ya lashe ba za a amince da shi ba, domin a baya ya amince da shan kaye.

Shekaru akalla 22 shugaba Jammeh ya yi yana mulkar kasar ta Gambia.

XS
SM
MD
LG